1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fadar Kremlin ta ce sai Ukraine ta sako mata mutanenta

Yusuf BalaMay 22, 2015

Mahukuntan Kiev sun kame mutane biyu bisa zargin cewa suna yaki cikin 'yan awaren na Ukraine da ke samun goyon bayan Rasha, abin da Moscow ke cewa da sakel.

https://p.dw.com/p/1FUWJ
Russland Putin Fragestunde
Hoto: Reuters/RIA Novosti/Kremlin/A. Druzhinin

Mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a ranar Jumma'ar nan cewa fadar ta Kremlin za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an sako mutanen nan biyu 'yan kasar ta Rasha da mahukuntan kasar Ukraine ke cewa sojojin kasar ne biyu da ta kama a matsayin fursinonin yaki.

Da yake jawabi ga manema labarai Dmitry Peskov ya ce wadannan mutane da aka kama hakika 'yan kasar ta Rasha ne kuma kasar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an sakosu.

Shi kuwa da yake nasa jawabin yayin halartar wani taro na kasashen EU a Latvia shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce kamata ya yi kasashen yamma su kara matsa lamba kan mahukuntan kasar ta Rasha:

"Abin da ke a zahiri shi ne batun mutunta yarejeniyar tsagaita wuta ta birnin Minsk da aka cimma babu ita, tamkar ba a yi ta ba, ba a kwashe baki dayan manyan kayan yaki ba da jibge a filin daga koda kuwa an kwashe to wasu 'yan kadan ne daga dukkanin bangarorin".