1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kutsen Rasha a Ukraine ya shiga makonni uku

Suleiman Babayo AH
March 16, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane milyan uku suka tsere zuwa gudun hijira sakamakon karfafa hare-hare da Rasha ta yi a kan Uraine yayin da yakin ya shiga makonni na uku.

https://p.dw.com/p/48Xel
Ukraine Kriegszerstörungen in Kiew
Hoto: Cover-Images/imago images

Rasha ta kara karfafa hare-hare kan birnin Kiev fadar gwamnatin Ukraine da birnin Mariupol gami da wasu manyan birane masu tasiri. Yayin da kutsen da Rasha ta kaddamar ya shiga makonni na uku sojojin na Rasha na ci gaba da neman ganin sun karbe iko da kasar sakamakon ci gaba da hare-hare babu kakkautawa.

Sai dai duk da yanayin da ake ciki Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar ta Ukraine ya ce har yanzu akwai sauran fata kan kulla yarjejeniya da gwamnatin Rasha. Kuma ya ce akwai haske kan tattaunawar da bangarorin biyu suka yi inda suke sake komawa kan teburin sulhu a wannan Laraba.

Sannan shugaban na Ukraine ya yi godiya wa AMirka kan sabon taimakon kudi na dala milyan dubu-13 da rabi wanda Shugaba Joe Biden na Amirka ya ayyawa Ukraine.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin fararen hula 700 suka mutu sakamakon hare-haren da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine, kuma akwai yuwuwar alkaluman za su haura haka. Kimanin mutane milyan uku sun tsere daga kasar zuwa gudun hijira kasashen ketere.