1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ci gaba da kai hare-hare gabashin Ukraine

Suleiman Babayo ATB
May 4, 2022

Hare-haren Rasha a gabashin Ukraine sun halaka mutane 21 yayin da wasu 28 suka jikata, yayin da shugaban Rasha ya nemi gani manyan kasashen sun katse taimakon Ukraine.

https://p.dw.com/p/4Anuh
Ukraine - Azovstal Stahlwerk in Mariupol stark beschädigt von russischen Angriffen
Hoto: picture alliance/dpa/TASS

Hare-haren da dakarun Rasha ke ci gaba da kai wa gabashin Ukraine sun yi sanadiyar mutuwar fararen hula fiye da 20 sannan wasu kimanin 30 suka jikata a yankin Donetsk.

Haka na zuwa lokacin da Shugaba Volodymyr Zelenksky na kasar ta Ukraine ya tabbatar da kwashe fiye da mutane 150 da suka makwale a garin Mariupol da aka yi wa kawanya.

Tuni Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bukaci Shugaba Emmanuel Macron na Fraansa da cewa ya dace kasashen Yammacin Duniya su daina bai wa Ukraine makamai, sannan ya zargi Ukraine da rashin daukan tattaunawa da muhimmanci.

Firaminista Boris Johnson na Birtaniya ya bayyana sabon shirin taimakon Ukraine da kimanin dala milyan 370, saboda ci gaba da nuna tirjiya ga Rasha.