Rasha ta tsare masu zanga-zanga | Siyasa | DW | 13.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rasha ta tsare masu zanga-zanga

Mahukuntan Rasha sun dauki matakan doka kan wadanda ke nuna kyamar gwamnatin shugaba Putin, inda suka tsare su. Daruruwan 'yan kasar ne dai suka gudanar da zanga-zangar da ta kai jami'an 'yan sanda nuna fushi tun farko.

A kasar Rasha wata kotun birnin Saint-Petersbourg ta yanke wa uku daga cikin masu zanga-zangar da aka kama hukuncin dauri na tsawon kwanaki goma-goma, da kuma tarar kudi ta Euro 156 kowanensu. Wannan ya biyo bayan wani hukuncin dauri na wata guda da ta yanke wa madugun 'yan adawar kasar Alexei Navalny.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan kamen mutane sama da dubu da 500 da jami'an 'yan sandan kasar ta Rasha suka gudanar a sakamakon wata zanga-zangar nuna kyama ga Shugaba Vladimir Putin da aka gudanar a birane da dama na kasar ta Rasha a kan kiran madugun 'yan adawar.

Kowanne daga cikin masu zanga-zangar da aka kama dai na iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na kwanaki 15 idan kotun ta tabbatar da laifin da ta ke zanginsu da aikatawa. Alexei Navalny madugun 'yan adawar kasar ta Rasha na sa ran kalubalantar Shugaba Putin a zaben shugaban kasa na watan Maris mai zuwa.