1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU. Takunkumi karo na tara ga Moscow

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 16, 2022

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta kakaba takunkumi karo na tara cikin wannan shekara a kan Rasha, sakamakon mamaye Ukraine da Moscow ta yi.

https://p.dw.com/p/4L586
Hukumar Tarayyar Turai  | Ursula von der Leyen | Takunkumi | Rasha | Ukraine
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen Hoto: Virginia Mayo/AP Photo/picture alliance

Shugabar Hukumar Tarayyar Turan Ursula von der Leyen ce ta sanar da matakin nasu a shafinta na Tiwitter, inda ta ce bangarorin da takunkumin ya shafa sun hadar da kamfanonin tsaro da bankuna da kafafen yada labarai da kuma wasu jami'an gwamnatin Rashan. A cewarta wannan wani mataki ne, na dakile karfin da Moscow ke da shi wajen ci gaba da yakin. von der Leyen ta kara da cewa, kusan daidaikun mutane 200 da ke da hannu wajen kai hare-hare a kan fararen hula da sace kananan yara a Ukraine takunkumin ya shafa. Za dai a hana wadanda abin ya shafa shiga kasashen EU, kana a toshe kadarorinsu da ke kasashe mambobin kungiyar. Kafafen yada labaran Rasha da takunkumin ya shafa sun hadar da, NTV/NTV Mir da Rossiya 1 da Pervyi Kanal da kuma REN TV. Haka kuma za a kara toshe wasu bankunan Rasha biyu da ke kasashen na EU, tare da shirin hana yin musayar kudi a bankin ci-gaba na Rasha da ke yankin wato Russian Regional Development Bank.