1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta sami goyon bayan majalisa, na amfani da dakarunta a Crimea

March 1, 2014

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya lashi takobin cewa duk wata shawara da aka yanke kan makomar Yukren ba zai shafi 'yan asalin ƙasarsa dake yankin ba.

https://p.dw.com/p/1BI39
Ukraine Russland Konflikt Krim 1. März 2014
Hoto: REUTERS

Majalisar dokokin Rasha ta amince da amfani da dakaru a tsibirin Crimea. Majalisar ta amince da buƙatar yin hakan ne da shugaban ƙasa Vladamir Putin ya gabatara mata.

A wata sanarwar da fadar Kremlin ta fitar, Putin ya bayyana cewa zai yi amfani da dakarun a ƙasar dake maƙotaka da ita har sai sadda fagen siyasarta ta sami daidaito.

Domin nuna goyon bayansu ga wannan buƙata da shugaba Putin ya bayar, majalisar ta kwatanta yanayin da ake ciki a Ukraine a matsayin wanda ya banbanta da duk waɗanda aka gani a baya, ta kuma ce babbar barazana ce ga 'yan asalin Rashar dake zaune a wurin.

Gwamnatin tsibirin Crimea dake goyon bayan matakin Rasha, da kuma jerin jiragen ruwan yaƙin Rashar da suke girke a tekun Bahr aswad sun amince su ba da haɗin kai.

To sai dai yau da rana da firaministan riƙon ƙasar Arseniy Yatsenyuk ke magana ya kwatanta cewa matakin Rasha ba zata firgita su ba

"kasancewar dakarun Rasha a Crimea ba wani abu bane illa tsokana, kuma duk wani yunƙurinta na jan Yukren cikin wani rikici ba zai yi tasiri ba"

Tuni dai ƙasashen duniya ke mayar da martani dangane da wannan batu inda shugaban Amirka Barack Obama shi ma ya yi tsokaci kamar haka

"Idan har aka take ikon cin gashin kan da Yukren ke da shi zai yi tasiri sosai ga makomar ƙasar, kuma tabbas Amirka za ta haɗa kai da al'ummar ƙasa da ƙasa wajen jaddada cewa ɗaukar matakin soji a Ukraine zai janyo martani

A cewar gwamnatin rikon kwaryar Yukren Rasha na da aƙalla dakaru 6000 a tsibirin Crimea.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu-Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar