Rasha ta nuna bacin ranta kan Amirka | Labarai | DW | 17.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta nuna bacin ranta kan Amirka

Rasha ta bukaci Amirka da ta mayar mata da ikon amfani da wasu sassan ofisoshin jakadancinta da ke wasu manyan biranen Amirkar, a dai dai lokacin da ake gab ta fara zama kan rigimar.

Kasar ta Rasha dai na matukar nuna bacin rai da matakin Amirka na hana jami'an diflomasiyyanta amfani da wasu gine-ginen jakadunta da ke a biranen New York da kuma Maryland.

Cikin watan Disambar bara ne dai tsohon shugaba Barack Obama ya bayar da umurnin rufe gidajen jami'an diflomasiyyan Rasha tare da korar 35 daga cikinsu, lokacin da ya yi zargin alamun kutsen da Rasha ke kokarin yi a zaben kasar da ya gabata.

Amirkar dai ta gindaya wasu sharuda ne na bude wuraren, sharudan da kuwa Rasha ke cewa ta yi hanzarin dage su ba tare da wani bata lokaci ba.