Rasha ta kori jami′an diflomasiyya na Jamus | Labarai | DW | 12.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta kori jami'an diflomasiyya na Jamus

Gwamnatin Jamus ta nuna damuwa kan matakin Rasha na sallamar jami'anta biyu, tare da gargadin wasu matakai masu zafi kan gwamnatin Moscow.

A wani mataki na ramuwar gayya gwamnatin Moscow ta ba wa jami'an diflomasiyya na Jamus biyu wa'adin kwanki bakwai su bar kasar, bayan korar nata jami'an a Berlin kan zargin kisan wani tsohon kwamandan sojin kasar Jojiya.

A makon jiya ne kasashen Rasha da Jamus suka fara sa-in-sa bayan Jamus ta zargi Moscow da hannu a kisan wani tsohon kwamandan sojin kasar jojiya a wurin shakatawa a birnin Berlin.