1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kori jami'an Birtaniya 23

Zainab Mohammed Abubakar
March 17, 2018

Rasha ta kuma dauki matakin rufe ofishin diplomasiyyar kasar da ke birnin Moscow, biyo bayan abun da ta kira" tunzurata" da Birtaniyar ta yi dangane da gubar da aka sawa tsohon jami'in leken asirinta da 'yarsa.

https://p.dw.com/p/2uW8s
Russland Sergej Lawrow in Moskau
Hoto: Reuters/A. Zemlianichenko

Ha'Ila yau, Moscow zata dakatar da dukkan ayyukan Birtaniya a kasar, wanda ke cikin jerin matakan martanin da ta gabatarwa jakadan kasar a Laurie Bristow a wannan Asabar din.

Sanarwar matakan da Rashan ta dauka na zuwa ne a jajiberin zaben shugaban kasa, da ake saran Vladimir Putin ne zai sake lashewa a karo na hudu, zaben da ke zuwa lokacin da aka mayar da Rashan tamkar saniyar ware. 

Wannan sabani ya samu asali ne bayan London ta zargi Moscow da alhakin sa wa tsohon jami'in Rashan Sergei Skripal da 'Yarsa Yulia guba tun a ranar 4 ga watan da muke ciki a birnin Salisbury, inda suke cikin matsanancin hali na jinya.