Rasha ta jaddada goyan baya ga Siriya | Labarai | DW | 01.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta jaddada goyan baya ga Siriya

Ministan harakokin wajen Rasha yace sabke Assad daga mulki ba shine hanyar warware rikicin ƙasar Siriya ba.

Syrian President Bashar Assad, right, meets with Russian Foreign Minister Sergey Lavrov in Damascus, Syria on Tuesday, Feb. 7, 2012. Syrian forces renewed their assault on the flashpoint city of Homs on Tuesday as Russia's foreign minister held talks in Damascus with President Bashar Assad about the country's escalating violence. (AP Photo, pool)

Sergei Lawrow da Assad

Shugaban komitin ƙoli na masu adawa da gwamnatin Siriya, ya zargi gamayyar ƙasa da ƙasa da nuna halayen ko in kula, game da kisan gillar da ya ce shugaba Bashar Al-Assad na aikatawa. Abdel Basset Saida, ya ce a yanzu Siriya ta zama wata mattatara ta masu tsatsauran kishin addinin Islama, dalili da ɗaukar sakainar kashi, da gamayyar ƙasa da ƙasa ke yi wa rikicin ƙasar.Basset Saida, ya jaddada kira ga ƙasashen duniya su baiwa 'yan tawayen Siriya tallafi, domin murƙushe dakarun gwamnati.

Saidai hata a jiya,a yayin wata ganawawa da ministan harkokin wajen Rasha yayi da takwaransa na Faransa, ya jaddada goya bayan Rasha ga gwamnatin Siriya, kuma Sergei Lavrov, ya yi fatali da bukatar ƙasashen Turai da Amurika, ta sabke shugaba Bashar Al-Assad.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu