1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta gargadi Turkiyya a kan Afrin

April 9, 2018

Gwamnatin kasar Rasha ta gargadin gwamnatin Turkiyya da ta hanzarta barin yankin Afrin da ke arewacin kasar Syria bayan cimma burin da ya kaita a can.

https://p.dw.com/p/2vk7y
Syrien Krieg Afrin | türkisches Militär
Hoto: Reuters/K. Ashawi

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya yi kira ga gwamnatin Turkiyya da ta janye daga yankin Afrin da ke arewacin Syria, tunda yake kasar ta cimma burinta a can. Kamfanin dillancin labaran Rashar ya ambato Mr. Lavrov na gargadin Shugaba Racep Tayyip Erdogan da ya guji mamaye yankin na Afrin ta hanyar kyale dakarunsa su ci gaba da zama babu wa'adi.

Su dai sojin na Turkiyya, sun kaddamar da sintiri ne a yankin na Afrin a cikin watan Janairu, abin da ya bude wani babin yaki a rigima a arewacin Syria da ke fama yaki tsawon shekaru bakwai cur. Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi kiyasin cewa akalla mutum dubu 167 suka rasa muhallansu a yankin na Afrin sakamakon farmakin na Turkiyya.