Rasha ta fara tura gas gabashin Ukraine | Labarai | DW | 19.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta fara tura gas gabashin Ukraine

Rahotanni daga gabashin Ukarine na cewar Rasha ta fara tura iskar gas zuwa yankunan da 'yan aware ke rike da su bayan da mahukunan Kiev suka dakatar da turawa yankin gas din.

Kamfanin dillancin labarai na RIA Novosti ya ce kamfanin na samar da makamashi musamman ma iskar gas wato Gazprom ya fara tura iskar gas din zuwa yankunan da suka hada Lugansk kamar yadda shugaban yankin ya shaida.

Gabannin haka firaministan Rasha din Dmitry Medvedev ya ce Moscow za ta agazawa yankunan gabashin Ukraine din da makamashi har ma ya bukaci ministan makamashin kasar da ya yi aiki tare da kamfanin na Gazprom don tabbatar da yiwuwar hakan.

Kiev dai ta ce ta katse tura isakar Gas zuwa yankunan da ke hannun 'yan tawayen ne saboda lalata bututun tura shi da aka yi sandaiyyar rikicin da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Rasha.