Rasha ta fara rage sojojinta a Siriya | Labarai | DW | 06.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta fara rage sojojinta a Siriya

Rasha ta fara rage sojojinta da kuma manyan makaman da ta jibge a gabashin Siriya a yakin da take da masu jihadi.

Kafofin yada labarai na Rasha sun ambato shugaban rundunar sojojin kasar yana mai cewar za a fara rage sojin ne da rukuni na farko na rudunar mayakan ruwa masu jiragen da ke dakon jiragen sama na  yaki da ke tashi daga gabashin gabar tekun Baharun don kai farmaki.A karshen watan Disamba na shekara da ta shige ne shugaban na Rasha Vladmir Putin ya baiyana sanarwa cewar za a soma rage addadin maykan na Rasha a Siriya.