1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta fara aiki da haramcin sayar da alkama.

August 15, 2010

Yau Rasha ta fara aiki da haramcin sayar da alkama ga ƙasashen ƙetare.

https://p.dw.com/p/Oo8z
Shugaba Dmitry Medvedev, ta hagu, a lokacin ganawarsa da wani darekton aikin noma.Hoto: AP

Yau Lahadi ne haramcin da hukumomin ƙasar Rasha suka sanya game da safarar alkama zuwa ƙasashe waje ke fara aiki, a daidai lokacin da ƙasar ke fafutukar shawo kan matsalar wutar dajin da ta lalata da dama daga cikin alkamar da ƙasar ta noma a bana. Hukumomin sun ɗauki matakin ne da nufin taƙaita tashin farashin kayayyakin masarufi a cikin gida, bayan ƙamfan ruwa mafi tsanani da ƙasar ta gani cikin fiye da shekaru 100, sakamakon wutar dajin da kuma ta jefa birnin Moscow, fadar gwamnatin ƙasar cikin hayaƙi. Muƙaddshin Firaministan ƙasar Rasha, Viktor Zubkov ya jaddada cewar, haramcin na wucin gadi ne, wanda za'a yi aiki da shi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba. Shugaban ƙasar ta Rasha, Dmitry Medvedev, ya ce akwai yiwuwar ɗage haramcin gabannin wa'adin da aka ajiye idan har amfanin gonar da aka girɓe ya wadata. Sai dai kuma Firaministan Rasha, Vladmir Putin ya yi gargadin cewar, mai yiwuwa wa'adin haramcin ya kai shekara ta 2011. Alƙaluma daga ma'aikatar kula da harkokin noma a ƙasar na nuni da cewar, ƙasar ba ta da alkamar da ta adana domin safararta zuwa ƙetare ko ma ta ɗage haramcin daga shekara ta 2011.Daga cikin ƙasashen da suka fi cin gajiyar alkamar da Rasha ke safararta zuwa ƙatare dai har da ƙasashen nahiyar Afirka da kuma gabashin Turai.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Halima Balaraba Abbas