Rasha ta ce Putin na cikin koshin lafiya | Labarai | DW | 16.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta ce Putin na cikin koshin lafiya

Rasha ta yi watsi da rade-radin da ake yi cewar rashin koshin lafiya ce sanya ba a ga shugaban kasar Vladmir Putin ba a bainar jama'a a tsawon kwanakin goman da suka gabata.

Fadar mulkin Rashan ta Kremlin ta ce wasu aiyyuka na daban ne suka sanya shugaban bai fito ba tsawon wadannan kwanaki inda ta fidda wasu hotunan bidiyo da ke nuna Putin din a wasu taruka da ya yi ko da dai wasu kafafen watsa labarai sun ce an dauki hotunan ne tun da jimawa.

Jingine wata ziyara da Shugaba Putin din ya yi zuwa kasar Kazakhstan a makon jiya ce ta sanya dasa ayar tambaya dangane da koshin lafiya amma wannan Litinin din an gashi tare da shugaban Kyrgyztan Almazbek Atanbayev a St. Petersberg kuma babu wata alama da ke nuna rashin lafiya a tattare da shi.