1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta baiyana kaduwa kan matakin da Ukraine

Zulaiha Abubakar
November 27, 2018

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya baiyana kaduwa game da matakin da kasar Ukraine zata dauka na amfani da dokar da zata ba da damar amfani da karfin sojoji biyo bayan rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/38xQK
Deutschland Treffen Angela Merkel Wladimir Putin auf Schloss Meseberg
Hoto: picture alliance/AA/A. Hosbas

Cikin wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Putin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a wannan Talatar, ya bukaci Jamus ta gargadi mahukuntan Ukraine kan abinda zai biyo baya matukar kasar ta cigaba da tsokanar Rasha.

A ranar Lahadin data gabata ne Rashar ta kame wasu jiragen ruwa uku mallakar kasar Ukraine bisa zargin su da tsallakawa iyakar ruwan Rasha lamarin da Ukraine ta aiyana da zalinci.