Rasha ta amince da tsagaita wuta a Siriya | Labarai | DW | 28.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta amince da tsagaita wuta a Siriya

Kasashen Turkiyya da Rasha sun amince da jadawalin yarjejeniya ta tsagaita wuta a daukacin kasar Siriya

Rasha da Turkiyya sun amince da shirin tsagaita wuta a fadin kasar Siriya. Yarjejeniyar dai za ta fara aiki ne a daren yau. Kafar yada labaran gwamnatin Turkiyya ta sanar a yau Laraba cewa Ankara da kuma Moscow suna kuma kara karfafa hadin kai domin kawo karshen yakin basasar Siriya. 

Kamfanin dillancin labaran Turkiyyar yace shirin ya kudiri fadada tsagaita wutar da Turkiyya da Rasha suka shiga tsakani a Aleppo a farkon wannan watan don kwashe fararen hula ya zuwa kasar baki daya. Ba'a dai fayyace inda aka cimma wannan yarjejeniya ba, sai dai an yi wasu tarukan tattaunawa a yan makonnin da suka gabata tsakanin Turkiyya da Rasha da kuma wakilan yan adawa a Ankara.