1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta shiga yakin Ukraine da Rasha

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 1, 2022

Ministan harkokin kasashen waje na Rasha Sergey Lavrov ya zargi kasashen yammacin duniya da shiga yakin da kasarsa ke yi da makwabciyarta Ukraine kai tsaye

https://p.dw.com/p/4KMTe
Rasha | Sergey Lavrov | Zargi | NATO | Yaki | Ukraine
Ministan harkokin kasashen waje na Rasha Sergey LavroHoto: Russian Foreign Ministry Press Service/AP/picture alliance

Ministan harkokin kasashen wajen na Rasha Sergey Lavrov ya ayyana bai wa Ukraine makamai dankuma bai wa sojojinta horo a matsayin dalilansa na yin wannan zargi. Lavrov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai ta hanyar kiran waya ta bidiyo, inda ya ce ba za a taba cewa Amirka da NATO ba su shiga cikin yakin dumu-dumu ba. Ya nunar da cewa kasashen Jamus da Birtaniya da Italiya, ba wai makamai kawai suke bai wa ssojojin Ukraine din ba har ma da ba su horo a cikin kasashensu.