Rasha na ci gaba da shisshigi a Ukraine | Labarai | DW | 04.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha na ci gaba da shisshigi a Ukraine

NATO ta ce har yanzu fadar mulki ta Moscow na samar wa 'yan awaren Ukraine da makamai tare da basu horon da suke bukata.

Kungiyar tsaro ta NATO ta zargi Rasha da ci gaba da marawa 'yan aware baya duk kuma da alkawarin da ta yi na bayar da hadin kai a kokarin da ake yi na kashe wutar rikicin da ke ci a gabashin Ukraine. Sakatare janar na wannan kungiya Jens Stoltenberg ya bayyana a lokacin wani taron manema labarai a birnin Bruxelles cewa fadar mulki ta Moscow ta na samar wa 'yan aware da makamai da kuma horon da suke bukata. Stoltenberg ya kuma nunar da cewar yanzu haka ma dai sojojin na Rasha na daf da isa kan iyakar kasarsu da Ukraine.

Tuni dai shugaba Petro Poroschenko na Ukraine ya baiwa rundunar sojin kasarsa umurnin tura dakaru don kare wasu biranen gabashin kasar daga hare-haren abokan gaba. Shi dai Poroschenko ya dauki wannan mataki ne yayin wani taron gaggawa na majalisar tsaro da ke zama na farko da aka shirya tun bayan zaben da aka gudanar da Donetsk da Lougansk.

Ukraine da kuma kasashen Turai sun danganta zaben da kafar angula ga shirin zaman lafiya. Yayin da Rasha ta yi na'am da shi, su kuma wadanda suka lashesu suka yi rantsuwar kama aiki a wannan Talatar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu