Rasha na bikin tunawa da karshen yakin duniya na II | Labarai | DW | 09.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha na bikin tunawa da karshen yakin duniya na II

Da dama dai shugabannin kasashen yamma da aka gaiyyata sun kaurace wa taron na ranar Asabar inda wasunsu suka tura wakilansu.

Russland Militärparade in Moskau

Dakarun sojan Rasha na fareti

Kasar Rasha a ranar Asabar din nan ta shirya wani gagarimin biki a dandalin Red Square inda a macin soji da ta shirya na ranar tara ga watan Mayu,take tuna nasararta kan dakarun 'yan Nazi 'na kasar Jamus shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu, kasar ta gwada irin sabbin makaman yaki da ta mallaka.

A cewar kafar samar da bayanan soji da ke fita mako-mako IHS, cikin irin tankokin yaki da kasar ke dasu yanzu, zai nuna irin sauyin da ta samu a fannin kera irin wadannan makamai daga na shekarun 1960 zuwa 1970.

A kwai ma jiragen yaki da aka tsara za su yi shawagi da nuna kwarewar soji a wajen wannan biki.

George Cotter, tsohon soja ne da ya hallacci yaki a wancan lokaci:

"Ni tsohon soja ne kuma wannan dama ce ta rayuwa a gareni na ga irin wadannan jiragen sama da suka kafa tarihi a Turai da yankin Pacific wannan waje shi ne ya dace mutum ya samu kansa a ranar irin ta yau".

Cikin makaman dai akwai wasu sabbin bindigogi da ke da karfin iya harba makamai masu linzami da suke iya sarrafa kansu, wani abu da ke nuna irin yadda kasar ta Rasha ke kara karfi wajen mallakar makamai da basa bukatar dan Adam ya sarrafasu.

Da dama dai shugabannin kasashen yamma sun kauracewa taron na ranar Asabar inda wasunsu suka tura wakilansu.