Rasha na barazanar kara dakaru a Kirimiya | Labarai | DW | 16.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha na barazanar kara dakaru a Kirimiya

Atisayen da Amirka da kawayenta suka kaddamar a yankin yammacin Ukraine ya sanya Rasha mayar da martani da barazanar tura dakarunta Kirimiya dan shirin ko ta kwana.

Rasha ta yi barazanar tura wasu karin dakaru zuwa sabuwar yankin da ta mayar nata wato Kirimiya, bayan da kungiyar kawancen tsaron NATO ta kaddamar da atisaye a yankin yammacin Ukraine, a yayin da dakarun gwamnatin Kiev ke yakar 'yan awaren da ke goyon bayan Rashar a yankin gabashin kasar.

Ministan tsaron Rashar Sergei Shoigu ya ce karuwar tashe-tashen hankula a Ukraine da ma kasancewar dakarun ketare a kusa da Rasha ne ya sanya wannan mataki ya zama tilas.

Ita dai gwamnati a Mosko ta na gargadin cewa wannan atisaye wanda za a gudanar har zuwa 26 ga watan Satumba, wanda kuma zai kunshi akalla dakaru dubu daya daga Amirka da kawayenta, na barazana ga yunkurin da ake yi na samar da zaman lafiya a yankin gabashin Ukraine, har ma da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma, wadda ke tangal-tangal a yanzu haka.

Kodashike, kungiyar kawanycen tsaron na NATo na zargin cewa ita kanta Rashar ta na da dakaru dubu daya, da daruruwan motocin yaki da bindigogin atillery a kasar, duk da cewa ta janye wasu daga cikin dakarun bayan da yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki ranar biyar ga wannan watan na Satumba da muke ciki.