1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: An tsare dubban magoya bayan Navalny

January 23, 2021

'Yan sanda sun kame mutane fiye da 2000 magoya bayan madugun adawa Alexei Navalny wadanda ke zanga zangar adawa da tsare yayin da kuma 'yan sanda 40 suka ji rauni a lokacin artabun a birnin Moscow.

https://p.dw.com/p/3oL9S
Russland Moskau | Proteste wegen Nawalny-Verhaftung
Hoto: Evgenia Novozhenina/REUTERS

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka wallafa faya-fayen da ke nuna yadda jami'an tsaron da suke rufe fuskokinsu tare da cin zarafin masu zanga-zangar.

Daruruwan mutane ne dai suka taru a tsakiyar birnin Moscow don gudanar da zanga-zanga, sai dai kuma hayaki mai sa hawaye da 'yan sanda suka harba ya haifar da arangama a tsakaninsu da masu zanga-zangar. 

Sai dai kuma wani na hannun daman madugun adawar da ke a tsare a yanzu Leonid Volkov ya ce 'yan adawa za su ci-gaba da gudanar da zanga-zangar a karshen mako mai zuwa don neman a saki Navalny.

Mutane fiye da 2000 ne aka kama a  ranar Asabar yayin zanga-zanga a sassan kasar ta Rasha wadanda ke nuna goyon baya ga madugun adawar Alexei Navalny.