1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaron Rasha sun tsare Alexei Navalny

Zulaiha Abubakar
August 25, 2018

Jami'an tsaro a kasar Rasha sun kame jagoran adawa Alexei Navalny yayin da ya ke kokarin shiga gidansa bayan sun kwace wayar sa ta hannu.

https://p.dw.com/p/33knQ
Russland Demo für freies Internet in Moskau | Navalny
Hoto: picture-alliance/dpa/TASS/M. Tereshchenko

Da ta ke zantawa da manema labarai mai magana da yawun jagoran 'yan adawar ta bayyana cewa kamen na sa ba zai rasa nasaba da shirin sa na gudanar da wata zanga-zangar a birnin Moscow da kuma wasu birane 100 a fadin kasar ta Rasha ba. Zanga-zangar dai na da alaka da kyamar da Navalny din ke da ita kan shirin gwamnatin kasar na kara shekarun yin ritaya daga aiki.