Rasha: A sagaita wuta a Ghouta | Labarai | DW | 27.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha: A sagaita wuta a Ghouta

Rasha ta bayar da umurnin tsagaita wuta na wani lokaci a kowace rana don bada damar shigar da kayan agaji a gabashin Ghouta, a hare-hare ta sama da dakarun gwamnatin Syria ke kaiwa a yankin.

Syrien Angriffe auf Ost-Ghuta (Reuters/B. Khabieh)

Halin da fararen hula ke ciki kenan a gabashin Ghouta na kasar Syria

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayar da umurnin takaita wuta na wani lokaci a kowace rana don bada damar shigar da kayan agaji a gabashin Ghouta, a hare-hare ta sama da dakarun gwamnatin Syria ke kaiwa a yankin. Umurnin shugaban na Rasha na zuwa ne rashin martaba amince wa tsagaita wuta da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi a ranar Asabar da ta gabata. Ana dai sa ran matakin tsagaita wutar zai fara aiki daga karfe 9 na safiya zuwa biyu na ranar wannan Talata don kai daukin ga wadanda ke cikin mawuyacin hali a gabashin na Ghouta.

Akalla fararen hula 550 hare-haren na gwamnatin Syria suka halaka cikin tsukin mako guda, hare-haren da jiragen Rasha ke kan gaba wajen kai su a cewar kungiyoyin duniya masu zaman kansu.  A cewar gwamnatin Syria dai ta tsaya ne don ganin ta murkushe mayakan tawaye da ke rike da yankin gabanin a kaiga tattaunawar zaman lafiya.