1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasa aikin yi bayan rushe Katangar Berlin

Ahmed Salisu
November 13, 2019

Yayin da ake ci gaba da bikin cika shekaru 30 da rushewar Katangar Berlin, ma’aikatan wata masana’anta da aka rufe a gashin kasar bayan rushe katangar na ci gaba da takaicin rasa aikinsu.

https://p.dw.com/p/3Snky
Themenreihe 25 Jahre Mauerfall Arbeitskampf von Bischofferode
Hoto: DW/F. Hentsch

Al’ummar Jamus na ci gaba da bukukuwa na murnar cika shekaru 30 da rushe Katangar Berlin wadda a baya ta raba Jamus ta Gabas da ta Yamma. Jami’an gwamnati ciki kuwa har da shugabar gwamnatin Angela Merkel da sauran ‘yan kasar ne suka halarci bukukuwa a birnin Berlin da sauran sassan kasar a ranar Asabar (09.11.2019).

To sai dai yayin da ake ci gaba da murnar zagayowar wannan rana, wasu kuwa nuna rashin jin dadinsu suke yi, musamman wadanda ke aiki a wasu daga cikin masana’atun da ke tsohuwar Jamus ta Gabas ciki kuwa har da ma’aikata masana’antar da ke sarrafa wani nau’i na gishiri da ake yin abubuwa da dama ciki har da takin zamani. Masana’antar da ke kauyen Bischofferode na garin Eichsfeld a jihar Thuringia ta kasance a kanun labarai saboda irin tada kayar bayan da aka rika yi har da yajin kin cin abinci lokacin da hukumomi suka ce za su rufeta.

Demonstration Bischofferode Kaliwerk
Ma'aikatan masana'antar sun yi yajin kin cin abinci kan batun rufe masana'antarsuHoto: picture-alliance/ZB

 

Hukumomi dai sun ce sun shirya rufe masana’antar ce saboda bukatar da ake da ita ta sinadarin da ta ke samarwa ya yi kasa sosai, sai dai ma’aikatan sun ce ba haka lamarin yake ba. Rufe masana’antar a shekarar 1993 ya sanya mutane da dama rasa aiyukansu yayin da garin ya kasance kamar kufai don mutanen da ke zaune duk sun fice. Bayan rufe masana’antar hukumomi sun yi wa ma’aikatan alkawarin ba su aiki da kuma biyansu diyya. Williband Nebel na daga cikin tsofaffin ma’aikatan masana’antar, ya kuma shaida cewar akwai da dama da ba a kai ga cikawa alkawarin da aka dauka ba don a cewarsa ‘an mana alkawari aiki amma a sani da na yi mutum 70 kawai aka samawa aiki daga cikin mutum 700‘‘.

Wannan yanayi da tsofaffin ma’aikatan wannan masana’anta suka shiga dai ya shafi yanayin siyasar yankin don a lokacin da wakilin DW Ahmed Salisu ya ziyarci kauyen da masana’atar take ya iske ana kakar zabe na jiha, kuma mafi akasarin fastoci da allunan ‘yan takara na jam’iyyun adawa ne ciki kuwa har da na masu kin jinin baki irin AfD. 

Bischofferode Kalibergbau
Williband Nebel da a baya ya yi aiki a masana'antar ya ce rufeta ya sauya alkiblar siyasar al'umma yankinHoto: DW/E. Bekele Tekle

Wannan sauyi da aka samu inji Williband Nebel ba zai ya rasa nasaba da irin abin da ya faru ga ma’aikatan masana’atarsu ba ko da dai shi ya ce ba shi da ra’ayin zabar AfD ko wata jam'iyya mai tsaurin ra'ayi. A cewarsa, karkatar da jama’a suka yi ga wasu jam’iyyun adawa ‘‘martanin ne da aka mayar game da batun na hadewar kasar bayan rushe bangon da ya rabata.‘‘