Rantsar da sabon shugaban Siri Lanka | Labarai | DW | 09.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rantsar da sabon shugaban Siri Lanka

Rantsar da Maithripala Sirisena na zuwa ne bayan doke abokin takararsa Mahinda Rajapakseya mai barin gado, wanda kuma ya amince da sakamakon.

A wannan Juma'arce ake rantsar da Maithripala Sirisena, a matsayin sabon shugaban kasar Siri Lanka, bayan doke shugaba maici, a wata fafatawa da suka yi a zaben kasar, da ya ta'allaka a kan zargin cin hanci da salon mulkin kama karya. Wani na hannu daman Mahinda Rajapakse, ya sanar da cewar shugaba mai barin gado, ya amince da sakamakon zaben. Ya kuma yi alkawarin mika mulki ga sabon shugaban kasar ba tare da wata matsala ba, a wani mataki da ya kira darajawa ra'ayin masu kada kuri'u. Sabon shugaban da ke zama tsohon ministan lafiya na Siri Lanka, ya samu nasarar ce sakamakon hadakar jam'iyyarsa ta adawa da sauran na kasar.