Ranar zaman lafia a duniya | Labarai | DW | 21.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar zaman lafia a duniya

A bangaren shagulgulan bukin ranar zaman lafiya ta duniya,sakatare general na mdd Ban Ki Moon yayi kira dangane da tsagaita wuta na yini guda ,a dukkan yankuna dake fama da rigingimu na tashe tashen hankula a sassa daban daban na duniya.Yace sa’oi 24 na zaman lafiya ,zai bawa mutane kwanciyar hankali ,tare da kawar dasu daga cikin yanayi na tsoro da rashin tsaro ,da miliyoyin mutane ke fama dashi.An dai kada kararrawar darajawa wannanrana ce yau a headquatar mdd,adaidai lokacin da shugabannin kasashen duniya ke hallara,domin bude mahawarrar majalisar na wannan shekara.Ana saran Ban zai jagorancin muhimman tattaunawa akan batutuwan Darfur da Iraki da Afganistan da kuma yankin gabas ta tsakiya.