Ranar yan gudun hijira ta dunia | Labarai | DW | 20.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar yan gudun hijira ta dunia

Yau ne ranar da Majalisar Ɗinkin Dunia ta ware, domin tuni da miliyoyin yan gudunn hijira da ke warwatse a ƙasashe daban-daban na dunia.

Albarkacin wannan rana, shugaban hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da yan gudun hijira, Antonio Guteres, ya ziyarci ƙasashen Cote d` Ivoire da Liberia, inda ya alƙawarta cewar, Majalisar a shire ta ke, ta yi jigillar yan gudun hijira Liberia, su kumanin dubu 250, dakuma samar masu ayyukan yi, domin sake gina wannan ƙasa da yaƙi ya ɗaiɗaita.

Antonio Guteres, da a halin yanzu ke birnin Monrobia, ya yi kira ga ƙasashe masu hannu da shuni, da su bada tallafin ya dace, domin cimma wannan buri.

Alƙalluman Majalisar Ɗinkin Dunia, sun nunar da cewa, a ƙalla yan dugun hijira,milion 8 da dubu ɗari 4, ke akwai a dunia baki ɗaya.

A duk faɗin dunia inji rahoton hukumar kulla da yan gudun hjira, ƙasar Afghanistan ta fi yawan bada mafaka, ga gudun hijira , inda a ƙalla su kussan million 2 da rabi su ka sami matsugunai, mafi yawan su, daga Pakistan da Iran.

Saidai a shekara bana,rahoton ya ce, an samu ragi na kashi 12 bisa 100, na yawan yan gudun hijira a dunia.