1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar yaki da azabtar da mata ta MDD

Zainab A MohammadNovember 25, 2005
https://p.dw.com/p/Bu3w
Mata daga sassan duniya
Mata daga sassan duniyaHoto: AP

25 ga watan Nuwamba na kowace shekara na mai kasancewa ran ace da majalisar dunkin duniya ta kebe domin nazari kan irin azaba da mata ke cigaba da fuskanta acikin gidajensu.Kamar kowace shekara hukumar kula da lafiya ta majalisar dunkin duniya ta gudanar bincike a kasashe masu yawa.

Rahotan da aka gabatar dangane da binciki kan bukin wannan rana ta wannan shekara,inda hukumar kula da lafiya ta mdd ta tattauna da mata dubu 24a kasashe daban daban guda 10,da suka hadar da Japan da Peru da Ethiopia da Newzealand da Serbia da Montenegro,na nuni dacewa mata na cigaba da fuskantar azabar cikin gida daga abokan zamansu,batu kuma da kan haifar da illa na lokaci mai tsawo a iya rayuwarsu matan.

Binciken dai ya tabbatar dacewa irin wannan azaba da ake gallazawa cikin gida shine yafi yawa daga cikin irin wahalhalu da mata ke fama dasu na rayuwa,kuma akasarinsu daga mazajen aurensu,ko kuma abokan zaman.

Akwai azabtarwa naui naui,wanda yakan danganta da kasa,alal misali abunda hukumar ta gano cewa azabtarwa ne a kasar Japan yasha banban da abunda ya kasancewa azabtar da matan dake kasar Habasha,kasar da kashi 50 daga cikin 100 na matansu na fama da azabtarwa daga mazajensu na aure acikin gida,batu da mai bincike ta mdd Henriette jansen ta bayyana takaicinta dashi kamar haka….

“abun ya tsoratad dani,domin ban taba zaton abubuwanda muka gano ba,domin sakamakon na nuni dacewa azaba da mata kasha ya zamanto ruwan dare,wanda yake faruwa akoina”.

Ita kuwa Claudia Garcia Moreno,Coorditatan hukumar kula da lafiyan , cewa tayi abun ya wuce misali tsakanin maaurata,domin ba abune na tunkude kai kadai ba,batu ne na aiwatar da lahani sosai wasu matan….

“Yawancin irin wadannan azabtarwa na jiki nayin tsamari.Muna Magana ne akan azaba na duka,da zai kai har ana jan mace a kasa,ko kuma konata walau da wayan lantarki,ko kuma da wuta na ainihi”.

Amma wani abun takaici dangane da irin wannan azaba da matan ke cigaba da fuskanta daga mazajensu na aure shine,illarsa wa lafiyar cikinsu.Akan hakane Henriette ta kara dacewa…

“Binciken namu ya gano cewa irin wadannan mata da mazajensu ke azabtarwa,sukan karasa rayuwarsu ne cikin hatsari na rashin koshin lafiya,ko kuma neman kashe kansu,da yawan barin ciki ,kana mai juna biyu sakamakon shan duka mai tsanani cikin datake dauke dashi na iya lalacewa.Adangane da haka azabtar da mata yana da illoli na lokaci mai tsawo a iyakar rayuwarta”.

Ita kuwa Moreno cewa tayi,abun tausayine a halin yanzu ganin cewa akasarin wadannan mata dake cikin wannan azaba,sun amince da yadda rayuwar take..

“Matan da kansu a wasu wurare sun amince dacewa dole ne a lakada mace duka a wasu lokuta kafin ta shiga hanya.Alal misali idan ta sabawa mijinta ta hanyar kin bin umurninsa,ko kuma idan shi mijin baya jin dadin yadda take tafiyar da harkokin gidansa”.

A dangane da hakane hukumar kula da lafiya ta mdd ta bukaci a horar da maaikatan kula da lafiya domin su rika laakari da irin wannan azabtar na cikin gida,musamman dangane da yadda zasu rika jinyan waddanda azabar ta ritsa dasu.Bugu da kari hukumar ta kumayi fatan cewa sakamakon wannan bincike da aka gabatar zai taimaka wajen fallasa irin azaba da mata ke cigaba da fuskanta acikin gidajensu na aure,domin daukan matakai na hukunci,saboda rashin dacewarsa,a kowane irin yanayi.