Ranar sallar ma´aikata ta dunia. | Labarai | DW | 01.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar sallar ma´aikata ta dunia.

Yau ne ma´aikata a dunia baki ɗaya ke shagulgulan salar ranar 1 ga watan Mai, da su ka saba yi, a kowace shekara, domin tunni, da mazajan farko, da su kayi famar yaƙi, don samar da yanci ga ma´aikata.

Ƙungiyoyin ƙwadago, na anfani da wanan dama , inda su ke issar da saƙwani zuwa ga magabata, a game da matalolin da ma´aikata ke fuskanta.

Saidai a shekara bana ,rahotani daga kasar Cambodge, sun ambata cewa,r da sanhin sahiyar yau, jami´an tsaro, su ka yi awan gaba, da shugaban babbar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, Chea Mony,a yayin da dubbunan ma´aikata, ke shirin gudanar da zanga zanga, a tsakiyar Phnom Penh babban birnin ƙasar.

Shaidu sun tabbatar da cewa, yan sanda, sun tassa ƙeyar sa, cikin motar su, a yayin da ya ke bukatar tantanawa tare da su, da nufin samar da izinin shigar masu zanga zangar, da su ka faro daga kewaye zuwa tsakiyar birnin.

Shugabaninj am´iyun adawa na ƙasa, a halin yanzu, sun fara kai da kawo, na neman belin Chea Mony.

Cambodge na ɗaya daga ƙasashen dunia, da su ka yi ƙaurin suna, ta fannin take haƙƙoƙin jama´a, da kuma takurawa ma´aikata.