Ranar Kiwon Lafiya Ta Duniya | Siyasa | DW | 06.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ranar Kiwon Lafiya Ta Duniya

A gobe alhamis MDD ke gabatar da bikinta na ranar kiwon lafiya ta duniya

Ita matsalar ta mace-macen yara da uwayensu, an taba mayar da hankali kanta a bikin da aka gabatar a shekara ta 1998. Matsalar haifuwa da mace-macen yara ko uwayen yaran abu ne dake damun kasashe masu tasowa matuka ainun. Mutane kan shiga dardar a duk lokacin da mace ke nakuda saboda rashin nagartaccen tsarin kiwon lafiya a kasashen da lamarin ya shafa. Dangane da kasashe masu kyakkyawan tsarin kiwon lafiya da kwararrun likitoci da unguwar-zuma kuwa lamarin ba haka yake ba, inda zaka tarar kome na tafiya salin alin kuma yaran da aka haifa su kan cimma shekaru biyar na haifuwa, wanda shi ne mizanin da aka tsayar na kiyasce yawan mace-macen yara a sassan duniya daban-daban. A lokacin da take bayani game da haka Joy Phumaphi, mataimakiyar darektan hukumar lafiya ta MDD WHO a takaice, ta ce wajibi ne a dauki kwararan matakai wajen magance wannan matsala. Uwayen yara da ‚ya’yansu kan sha fama da radadi da mace-mace a duk shekara. Akwai bukatar daukar kwararan matakai a game da haka. Domin kuwa maganan nan da muke yi yanzu haka akwai mata dake asarar rayukansu ko kuma barin ‚ya’yansu a bayan kowace dakika daya. Wannan ba abu ne da duniya zata lamunce masa ba. Kazalika ba za a lamunta da gaskiyar cewa a duk shekara jarirai miliyan hudu kan yi asarar rayukansu, kafin su samu makonni hudu da haifuwa, sakamakon wasu cuttukan da ba su gagari magani ba. A baya ga haka akwai wasu cututtuka na annoba da kan halaka yara miliyan 11 a shekara tun kafin su samu shekaru biyar da haifuwa. A gobe alhamis ne hukumar lafiya ta MDD zata gabatar da sabuwar kididdigarta a game da irin ci gaban da ake samu a al’amuran kiwon lafiya. To sai dai kuma tuntuni aka hakikance cewar akwai kakkarfar dangantaka tsakanin matsalar talauci da ta ta ilimi da kuma mace-macen yara da uwayensu. A karkashin kudurin da kasashe 189 suka cimma dangane da sabon karnin nan da muke ciki ana fatan kayyade matsalar mace-macen uwayen yara nan da shekara ta 2015. Amma da wuya a iya cimma wannan buri ta la’akari da karancin kudin da ake fama da shi kamar yadda aka ji daga Joy Phumaphi. Bisa ga ra’ayinta bai kamata taimakon da kasashe masu ci gaban masana’antu ke bayarwa ya ta’allaka kawai akan manufofi na jinkai ko tausayawa ba, wajibi ne su ba da la’akari ga makomar rayuwar dan-Adam baki daya, saboda wadannan yara fa su ne manyan gobe kuma akansu za a dogara a dukkan fannoni na rayuwa.