Rana ta karshe a babban taron Afirka a Bonn | Labarai | DW | 06.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rana ta karshe a babban taron Afirka a Bonn

An shiga rana ta biyu kuma ta karshe a babban taron yini biyu akan nahiyar Afirka dake gudana a masaukin manyan bakin gwamnatin Jamus na Petersberg dake nan birnin Bonn don tattauna sabbbin hanyoyin da za´a bi don inganta manufofin raya kasashe masu tasowa. Taron mai taken Kawance da Afirka, wani sabon shiri ne na shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler da nufin ba kasashen nahiyar Afirka damar fada a ji a manufofin raya kasashe matalauta. Rahotanni daga zauren taron sun ce yanzu haka ana nan ana tattaunawa shugaba Köhler da shugaban ATK Thabo Mbeki da takwaransa na Nijeriya Olusegun Obasanjo da kuma FM Habasha Meles Zenawi, musamman akan huldar dangantaku tsakanin Jamus da kasashen Afirka.