1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rana ta biyu a taron kolin kungiyar Commonwealth a tsibirin Malta

November 26, 2005
https://p.dw.com/p/BvJR

Damuwar da ake nunawa game da kasar Uganda ita ce ta dabaibaye rana ta farko a taron yini 3 na kasashen kungiyar Commonwealth da aka fara jiya juma´a a Valetta babban birnin kasar Malta. Shugabannin kasashe 53 na kungiyar kasashen da suka taba zama karkashin mulkin mallakar Birtaniya sun nemi bayani game da tsare shugaban ´yan adawa bisa zargin cin amanar kasa. Matsin lambar da ya sha daga kasashen duniya ya tilasta shugaban Uganda Yoweri Museveni kiran wani taron manema labarai don yin watsi da zargin da aka yi cewar kame Kizza Besigye na da wata manufa ta siyasa. Museveni ya jaddada cewar ba zai hana Besigye tsayawa takara a zaben shugaban kasar da ke tafe ba.