1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rana dai bata karya a zaben Amurka

November 5, 2012

Bayan kampe na lokaci mai tsawo da muhawarori, yan takara a zaben shugaban Amurka zasu fuskanci masu kada kuri'u ranar Talata

https://p.dw.com/p/16dIJ
Hoto: Reuters

'Yan takarar Amurka masu zawarcin kujerar shugaban kasa sun shiga mataki na karshe a yakin neman zabe, yayin da a gobe ne milyoyin 'yan kasar za su zabi mutumen da ya dace musu ga kasancewa shugaban kasa tsakanin dan takar Republikan bugu da kari tsohon gwamnan jihar Massachusetts Mitt Romney da kuma shugaba mai bari gado daga jam'iyar Demokrat Barack Obama. Isshu Maman ya hada muna rahoto a kan yunkurin da 'yan takarar ke yi na shawo kan masu kada kuri'ar.

Yadda magoya bayan 'yan takarar ke soya tare da rera wakoki ga 'yan takarar guda biyu.

A bisa al'ada dai kasar Amurka na zaben shugaban kasa ne a ranar Talata ta farko na kowane wata Nuwamba inda masu kada kuri'u ke amfani da takardun zaben shugaban kasa da na wakilan zauren shawara,da na majalisar dattawa har ma da na kananan hukumomi. A ranar Talata ne idan Allah ya kai mu miliyoyin Amurkawan ke kada kuri'unsu da nufin zaben shugaban kasar na 13 tun bayan kammala yakin duniya na biyu. Daga cikin shuwagabanin da suka jagorancin kasar tun a wannan lokacin sun hada da Demokrat 7 yayin da aka samu Republikan 7. Yanzu haka dai bisa ga yadda rahotanin kiddidiga ke zuwa, shugaba Obama ne ke kan gaba da takaitacen rinjaye. Kamar dai yadda ya saba,ko a yau din, abokin hamayar shugaban kasar wato Romney, ya kalubalanci Obama a kan tsarinsa na yakin neman zabe, inda ya ce mun ji ana yawan amfani da kalmar canji, to amman shugaban kasa ya dau arkawura da dama ba tare da ya cika su.

"Ya ce canjin da muke jin ana yawan kira,canji da ake bugun kirji da shi,mu gare mu canji abu ne da za a iya aunawa da fatar baki. To amman ainahin canji ana auna shi ne da irin ci-gaba da nasararorin da aka samu. Shekaru 4 da suka gabata,dan takara Obama ya dau alkawuran da ya sake cikawa ."

To shi ma dai shugaban kasar a lokacin da ya ke maida martani, bai yi kasa a gwiwa ba gurin kalubalantar yadda dan takarar republikan ke yakin neman zaben tare kuma da bada hasken irin halin da ya karbi ragamar iko.

USA US Wahl 2012 Wahlkampf 04.11.
Magoya bayan Barack Obama a kampeHoto: Reuters

"A shekara ta 2008,muna cikin wani irin matsanancin halin tattalin arziki kwatankwacin yadda aka taba fuskantar shekaru da dama da suka wuce a can baya. To amman a halin yanzu,mun samar da habbakar tattalin arzikin Amurka wadda yazu ta dawo sahun kasashe masu karfin arziki da ci-gaba."

Yanzu haka dai duk da ragowar karfin magoya bbaya da ake gani shugaban ya samu bisa ga la'akari ga shekru 4 da suka wuce a lokacin yakin neman zabe,shugaban na ci gaba da samun kwarin gwiwa inda tsohon shugaban kasar dan jam'iyar demokrat Bill Clinton ya nuna a fili goyon bayan sa ga dan takarar jam'iyarsu.

Su ma magoya bayan nasu na ci-gaba da yakin neman zabe ga 'yan takarar nasu daban daban kamar yadda wannan mata da ke goyon bayan Ramney ke cewa:

"Ta ce ni na dawo daga rakiyar masu launi bula a can baya su ne ni zaba yanzu kuma masu ja za kadawa kuri'a. Har yanzu dangina da abukanina na cikin wahala,ba Amurkan da ni girma cikinta ce ba."

Mata dai na nufin masui launin bula wato demokrat yayinda ta ke magana da masu ja a matsayin republikan. Ita ma wannan matar da ke bayana ra'ayinta jim kadan bayan da ta fito daga taron gangamin da shugaba Obama ya shirya yau da safe a jihar New Hampshire cewa ta yi.

USA US Wahl 2012 Wahlkampf 04.11.
Dan takara na jam'iyar Republicans Mitt RomneyHoto: EMMANUEL DUNAND/AFP/Getty Images

" Yana da tsari mai inganci,kuma kun san shi dan talaka ne ba a haife shi da zinari a hannu ba,don haka Obama ya san halin da masu karamin karfi ke ciki."

Wata daya da ya shude kimanin 'yan kasar Amurkan miliyon 19 ne suka kada kuri'unsu a wani matakin da wasu ke kallo a matsayin riga mallan shuiga masallaci. To dama dai kundin tsarin milkin kasar ya tanadin irin wannan sha'ani domin baiwa wadanda basu dama ranar zabe cika aikin su na 'yan kasa. Sanin kowa ne cewa a kasar Amurka,ba a bayana ranaikun zabe ba a kasar a matsayin ranaikun hutu. ko mi a ke ciki dai hausawa kan ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu