Ramaphosa: Za a binciki masu fariya da dukiya | Labarai | DW | 21.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ramaphosa: Za a binciki masu fariya da dukiya

Sabon shugaban kasa a Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a ranar Talata ya fada wa 'yan majalisar dokokin kasar cewa lokaci ya yi da za a fara bin diddigi kan irin rayuwar da masu rike da madafun iko suke yi.

A cewar shugaban wannan mataki zai taimaka wa kasar ta Afirka ta Kudu a kokarin da ta sanya a gaba na yaki da cin hanci da rashawa.

Jam'iyyar ANC mai mulki dai ta bijiro da tsare-tsare na hanyoyin yaki da cin hanci inda a ka bukaci kwararru da hukumomi masu sa ido su shiga aiki ka'in da-na-in ta yadda za a zakulo mutanen da ke tafiyar da tsarin rayuwa da ta saba wa ka'ida ko ta almubazzaranci ta yadda za a yi bincike ko gurfanar da duk wadanda aka samu da aikata duk wani nau'i na cin hanci da rashawa.