Rahoton UNICEF kan yi wa mata kaciya a duniya | Labarai | DW | 05.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoton UNICEF kan yi wa mata kaciya a duniya

A kalla mata miliyan 200 ne a duniya ke fama da matsalar kaciya da aka yi musu kuma akasarinsu na cikin kasashe kamar su Masar, Habasha da Indonesiya.

Rahoton ya ce kasashe kamar su Somaliya, Gini da Jibuti sun kasance inda wannan dabi'a ta yi kamari. Amma kuma wannan adadin ya rage a kasashe kamar Laberiya, Burkina Faso da kuma a kasar Kenya. Rahoton ya kara da cewa daga cikin mutane miliyan 200, miliyan 44 dukanninsu 'yan mata ne 'yan kasa da shekara 14, kuma daga cikin kasashe 30 inda ake wannan dabi'a, akasarin 'yan matan ana yi musu kaciyar ne tun kafin su kai shekaru biyar da aihuwa.