1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Shekara Na Kungiyar Taimakon Fasaha Ta Jamus GTZ

May 25, 2004

A cikin alfahari da murna kungiyar taimakon fasaha ta Jamus GTZ ta gabatar da rahoto akan ayyukanta dangane da shekara ta 2003

https://p.dw.com/p/BvjK
Tutar Kungiyar Taimakon Fasaha Ta Jamus GTZ
Tutar Kungiyar Taimakon Fasaha Ta Jamus GTZ

Kungiyar taimakon fasaha ta Jamus GTZ, ta bayyana alfaharinta a game da ayyukan da ta gabatar a shekarar da ta wuce. Domin kuwa a jerin kungiyoyin taimako na kasa da kasa da Bankin Duniya ya lissafta, kungiyar ce tayi ta daya a tsakanin dukkan kungiyoyin taimako na kasashen G7 da suka fi ci gaban masana’antu a duniya. Kungiyar kazalika ta taka rawar gani a ayyukan taimakon raya kasashe masu tasowa, a cewar Wolfgang Schmitt, darektar kungiyar a lokacin bikin gabatar da rahotonta na shekara. Kungiyar ta samu lambar yabo ta gamayyar tituna ta kasa da kasa, sakamakon gudummawar da ta bayar wajen kyautata makomar tituna a kasashe goma na yankin Latin Amurka. A yayinda a bangare guda tayi cinikin abin da ya kai Euro miliyan 900, a daya bangaren kuma ta samu kwangilar da ta kai ta kusan Euro miliyan dubu daya, galibi daga wasu kafofi na gwamnatin tarayya, musamman ma ma’aikatar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus. Wani abin alfahari gareta kuma shi ne kwangilar da take samu daga kasashe na ketare da cibiyoyin kudi na kasa da kasa. A wannan bangaren kungiyar GTZ tayi cinikin abin da ya kai Euro miliyan 123. Gaba daya GTZ ta tafiyar da shirye-shiryen rayawa kimanin 2700 a kasashe 131 a shekarar da ta wuce. Daya daga cikin wuraren da suka fi daukar hankali dangane da ayyukan cibiyar mai kwararrun ma’aikata 1000 a shelkwatarta dake garin Eschborn, ita ce kasar Afghanistan. Kungiyar ta ba da kakkarfar gudummawa wajen hada kan wakilan Loya Jirga da ta hada illahirin shuagabannin kabilun kasar kuma tana bakin kokarinta wajen sake farfado da hanyoyin sadarwa a sauran yankunanta. A lokacin da yake bayani game da ayyukan kungiyar ta GTZ a Afghanistan, shugaban kwamitinta na zartaswa kuma karamin minista a ma’aikatar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Erich Stather yayi nuni da irin banbance-banbancen ra’ayin da aka samu tsakanin kungiyar da wakilan rundunar sojan Jamus da aka tsugunar a Afghanistan, inda ya ci gaba da cewar:

Ko tantama babu a game da cewar sojojin na da ikon gina rijiyoyi, kamar yadda suke tattare da imani, amma abin dake akwai shi ne wadannan rijiyoyi ba zasu yi karko ba, saboda ba su da wata masniya a game da haka. A irin wannan mataki tilas ne kwararrun ma’aikatanmu su sa baki su nuna wa sojojin hanyoyin gina rijiyoyi masu karko.

Kazalika an fuskanci sabani tare da sojojin na Jamus dangane da inda za a yi wa kwararrun ma’aikata na kungiyar ta GTZ muhallin zama. a yayinda sojojin ke dagewa akan lalle sai ma’aikata su ci gaba da zama a barikokin da suka tanadar, su kuma ma’aikatan a nasu bangaren sai suka fi kaunar su zauna a wani gida na haya tare da ‚yan gadi fararen kaya. Hakan kuwa ya taimaka ma’aikatan suka tsira daga hare-haren da aka fuskanci sansanonin sojan da su.