1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

260608 Welt-Katastrophenbericht AIDS

Lechler, Pascal / Genf (MDR) June 26, 2008

Rahoton ya mayar da hankali kan cutar AIDS ko Sida

https://p.dw.com/p/ERZ7
AIDS a AfirkaHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce annobar cutar AIDS ko Sida a Afirka ta yi ƙamari ta yadda za a iya kwatanta ta da wani bala´i shigen ambaliyar ruwa ko matsananciyar yunwa. A cikin rahotonta na shekara game da Bala´o´i a Duniya, tarayyar ƙungiyar Red Cross da Red Crescent ta ce ko shakka babu cutar HIV/AIDS ta yi daidai da ma´anar da majalisar ɗinkin duniya ta bawa kalmar bala´i.


Wannan dai shi ne karon farko da wani rahoto dangane da bala´o´i a duniya ya mayar da hankali kan wata cuta guda ɗaya wato AIDS a wannan karo. A kowace shekara tarayyar ƙungiyar agaji ta Red Cross da ke zama uwar ƙungiyoyin agaji 186 tana ba da rahoto dangane da bala´o´i a duniya. A lokacin da yake magana a birnin Geneva shugaban tarayyar Ibrahim Osman ya ba dalilin da ya sa cutar AIDS ta zama jigon rahoton a bana.


Ya ce "Duk da cewa kowa na magana game da AIDS amma har yanzu cutar na zaman gagara-badau, inda take ci-gaba da addabar mutane musammman a yankunan da a da ma suka kasance mafi haɗari a duniya wato kamar ƙasashen Afirka kudu da Sahara. Mun mayar da AIDS jigon rahotonmu ne domin ƙara janyo hankalin jama´a su canza tunaninsu kan tinkarar wannan matsala."


Cutar ta zama wani bala´i a ƙasashen Afirka na kudu da Sahara, inda kashi ɗaya bisa biyar na al´ummomin yankin suka kamu ƙwayoyin HIV mai haddasa AIDS cutar dake kan gaba wajen zama sanadiyar mutuwar miliyoyin mutane. To amma duk da haka an samu ci-gaba misali a ƙasar Kenya inda a cikin shekaru 16 yawan masu ɗauke da cutar ya ragu da kimanin kashi 50 cikin 100. To sai dai kuma murna ka iya komawa ciki dangane da nasarorin da gwamnatin Kenya ta samu wajen yaƙi da cutar ta AIDS sakamakon rikicin siyasa biyowa bayan zaɓen shugaban ƙasar a ƙarshen shekara ta 2007. Lindsay Knight ɗaya daga cikin mutanen da suka rubuta rahoton ta ce ƙasar Kenya kyakkyawan misali ce yadda rikicin siyasa ko bala´o´i daga Indallahi ke iya mayar da hannun agogo baya a yaƙin da ake yi da AIDS.


Ta ce "Ma´aikatan agaji ba su iya ba da wani taimako a cikin wani mawuyacin hali da aka shiga sakamakon rigingimu. An yi ta yiwa mata da ƙananan yara fyaɗe ba tare da wata kariya ba. Wato kenan bala´o´i ka iya haddasa yaɗuwar AIDS."


A nan nahiyar Turai kuwa AIDS ta fi yaɗuwa a ƙasashen Rasha da Ukraine inda kimanin kashi 70 cikin 100 na masu shan miyagun ƙwayoyi suka kamu da cutar. Waɗannan ƙasashen biyu na zama misali kan yadda ake mayar da marasa galihu saniyar ware a matakan rigakafin kamuwa da AIDS.


Ban da cutar AIDS rahoton ya kuma yi tsokaci akan bala´o´i iri daban daban, inda a bara aka samu aukuwar bala´o´i kimanin 400 idan aka kwatanta da 420 a bara waccan. Sannan yawan waɗanda suka mutu sakamakon bala´o´in shi ne mafi ƙaranci a cikin shekaru 10. Amma yawan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon aukuwar girgizar ƙasa ko mahaukaciyar guguwa ko ambaliyar ruwa ya ƙaru da kashi 40 cikin 100.