Rahoton nazarin makomar Iraqi ya bukaci tattaunawa da Iran da Syria | Labarai | DW | 07.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoton nazarin makomar Iraqi ya bukaci tattaunawa da Iran da Syria

Rahoton komitin manyan mutane da sukayi nazarin makomar Iraqin karkashin tsohon sakataren tsaro James Baker da Lee Hamilton tsohon dan majalisa na Rep. Yace hanyar diplomasiya ce kadai zata magance halinda ake ciki a Iraqi.

Ya kuma shawarta tattaunawa da abokan gabar Amurka 2 wato Syria da Iran,

rahoton yace ya kamata Amurka da sauran manyan kasashen duniya su kafa wata kungiya ta taimakon kasa da kasa wadda zata sanya kasashen Syria da Iran cikin tattaunawar kawo karshen rikici a Iraqi.

Yace dole ne Amurkan ta tattauna da abokan gabarta muddin dai tana bukatar magance rikici da ake ciki.

Rahoton ya zargi kasashen 2 na Syria da Iran da laifin kara dagula alamaura a kasar Iraqi.