RAHOTON KARSHEMN SHEKARA NA 2003 NA HUKUMAR WHO | Siyasa | DW | 18.12.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

RAHOTON KARSHEMN SHEKARA NA 2003 NA HUKUMAR WHO

A cikin rahoton karshen shekarar ta 2003 hukumar lafiyar ta duniya ta godewa Allah kann irin hikimar daya bawa kwararrun likitocin ta na kwazon da suka nuna danane da shawo kann cutar nan data addabi mutanen duniya,musanmamma na kasashen Asia wato Sars. Cutar Sars, mai kama da matsananciyar murna wacce ke toshe jijiyoyin numfashi na Dan adam,a cewar rahoton na Who ta matukar buwayi kasashe da daman gaske na duniya,to amma asalin cutar a cewar rahoton ta samo asali ne daga kudancin kasar sin a karshen shekarar 2002,wanda bullar ta keda wuya ta harbi mutane dubu takwas a kasashe 32 na duniya,kana a hannu daya tayi sanadiyyar rayukan mutane 800,amma da yawan su mutanen da suka fito ne daga kasashen Asiya.

Bugu da kari rahoton na Who ya kuma kara da cewa kasashen da wannan cuta ta bula a cikin su da kuma basu da kyakkyawan tsarin inganta harkar lafiya sun kawowa hukumar matsala kwarai da gaske wajen dakile yaduwar wannan cuta a doron duniya baki daya. A wata sabuwa kuma hukumar ta Who ta kara da cewa, da ace cutar ta Sars ta samu gindin zama a wasu kasashe na Africa da basu da ingantaccen tsarin kiyopn lafiya da ba,a san yadda zata kasance ba,dangane da yadda cutar zata dinga yin fyadar yayan kadanya na rayukan bayin Allah a irin wadan nan kasashe. TO amma duk da haka a cewar hukumar ta Who ta hanyar mayar da hankali da kuma bincike bincike kwararrun likitocin hukumar sun samu galabar shawo kann wannan cuta data sako mutanen duniya a gaba. Har ila yau rahoton yayi karin haske da cewa ya samu darasi mai dinbin gaske dangane da ballewar wannan cuta,musanmamma daga watan Nuwanba na shekarar 2002 zuwa watan yuli na shekarar 2003,dangane da yadda ya kamata da dauki matakan rigakafi naci gaba da yaduwar cutar da kuma ma wasu cututtukan na daban dake barazana ga rayukan alummar duniya. A daya hannun kuma hukumar ta Lafiya ta duniya ta kuma yi karin haske tare da janyo hankulan gwamnatocin kasashe dasu lura da inganta kiyon lafiyar mutanen kasashen su tare da tsabtace muhalli,don yin hannun riga da ire iren wadan nan cututtuka na zamani. A karshe rahoton ya nunar da cewa hukumar Ta Who zataci gaba da gudanar da bincike dangane da yadda za,a kawo karshen wannan cuta a doron kasa baki daya tare da wasu cututtukan dake kawo baraza ga rayuwar bil adama.