1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton hadarin jirgin Germanwings

Yusuf BalaMarch 13, 2016

Masu binciken na birnin Paris sun yi amannar cewar mataimakin matukin jirgin saman na Germanwings ne ya kulle kansa ya saita jirgin ya yi hadari.

https://p.dw.com/p/1ICPn
Airbus A320 Cockpit
Sashin da direban jirgi ke zamaHoto: picture alliance/landov

Bayan kusan shekara guda da jirgin Germanwings mai lamba 4U 9525 daga birnin Barcelona zuwa Düsseldorf da fasinja 150 ya yi hadari ya kuma kashe daukacin fasinjansa, a ranar Lahadin nan ma'aikatar harkokin sufurin jiragen sama ta kasar Faransa ta fitar da sakamakon bincikenta.

Masu binciken na birnin Paris sun yi amannar cewar mataimakin matukin jirgin Andreas Lubitz ya kulle kansa a wajen da ake sarrafa jirgin inda ya saita shi dan ya tunkari inda tsaunikan suke, a hadarin da ya faru a ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2015. Sannan a cewar rahoton direban jirgin na zuwa ganin likita an kuma tura shi ya ga likitan kwakwalwa sati biyu kafin hadarin.

Tambayar Christof Wellens, da ke zama lauya mai kare iyalan wadanda suka rasu daga Jamus ita ce mai yasa mutum da ke cikin dimuwa zai ja jirgin fasinja. Sai dai a cewar mai gabatar da kara a Marseille karkashin dokoki na Jamus koda likitocin sun gano matsalar tasa ba za su bayyana wa wadanda suka dauke shi aiki ba.

Masu binciken dai na Faransa sun bukaci daga lokaci zuwa lokaci a rika gwajin lafiyar kwakwalwa ta matuka jiragen na sama.