Rahoton CIA ya zama abin kunyar Amirka | Labarai | DW | 09.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoton CIA ya zama abin kunyar Amirka

Gallazawar da ake amfani da ita dan tatsar bayanai ta wuce kima wanda bayan wadanda aka kama ana zargi da ayyukan ta'addanci harma iyalansu ana musu barazana.

CIA Folter Report Senatorin Dianne Feinstein

Sanata Dianne Feinstein: shugabar kwamitin binciken CIA

Shugaba Barack Obama na Amirka ya bayyana hanyar da jami'an leken asiri na (CIA) ke bi wajen tatsar bayanai da cewa hanya ce mai haifar da rudani, shugaban ya bayyana haka ne bayan da kwamitin binciken sirri a majalisar dokokin kasar da aka bawa alhakin gudanar da wannan aiki kan cibiyar ya fitar da rahotansa a ranar Talatannan.

Ya ce rahoton ya tabbatar da tsawon lokaci da yayi yana nazari cewa wannan hanya mai tsauri ba ta dace ba da irin martabar kasar ta Amirka, ba su da ce ba kuma da irin yadda suke so su tatsi bayanai a kokarin yaki da ta'addanci da ma tsaron da kasar ta Amirka ke da shi.

Sanata Dianne Feinstein, ita ta jagoranci wannan kwamitin bincike:

"Rahoton ya yi nazari kan yadda CIA ta yi amfani da wannan hanya mai cike da gallazawa wajen neman bayanai ga wasu mutane 119. Cikin makonni da suka gabata na samu kaina cikin wani yanayi na tunanin ko ma dai kada na bada rahoton sai a nan gaba".

Shugaba Obama ya ce hanyar tatsar bayanan bama kawai zubar da kimar kasar ta Amirka ba a idon duniya, hakan ya sanya basa samun hadin kai kan muradunsu da kawayensu cikin sauki.

A karshe dai shugaba Obama ya yi alkawarin cewa rahoton da ya fita yana fatan zai sanya a watsar da irin wannan hanyoyi da cibiyar ta leken asiri ta CIA ke amfani da su a baya.