1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Ƙungiyar Transperancy kan cin hanci da rashawa

Salissou BoukariNovember 17, 2009

Transparency International tace ƙasashe matalauta sune ke fama da matsalar cin hanci da rashawa.

https://p.dw.com/p/KZNW
Tambarin Transparency International

ƙungiyar mai cibiya a birnin Berlin na nan ƙasar Jamus, tace ƙasashe matalauta da wa'inda yaƙi ya ɗaiɗaita sune sukafi fama da matsalar cin hanci kamar musali ƙasashen, Afghanistan, Somaliya,Sudan da Iraki.

Saidai saɓanin wa'innan ƙasashe, su kuma ƙasashe kamar su New Zelande, Danemark, Singapour, sun kasance ƙashe uku da sukafi rishin wannan matsala ta cin hanci da rashawa, a cewar sakamakon bincike har kashi goma sha uku(13) da ƙungiyoyi daban daban har guda goma suka gudanar a cikin ƙasashe ɗari da tamanin(180) na duniya.

Da take amsa tambaya a game da rikicin tattalin arziki da ake fama da shi ya shafi matsalar cin hanci a Jamus, shugabar ƙungiyar Transparency reshen Jamus, Sylvia Schenk tace:

Kamar yadda kusan ko wane masani yake shaida mana,muna iya ɗaukar cewa rikicin tattalin arziki da ake fama da shi, ya ƙara tsananta yiyuwar samun ƙaruwar cin hanci a nan Jamus, musamman ma soboda ganin cewar kampononi da masana'antu suna ɗaukar matakai ko ta halin ƙaƙa su sami yadda zasuyi cinikin kayayakin su, saboda basa tambayar yadda aka kai ga sayan wa'innan kayayaki. Bugu da ƙari kuma, kampanoni da masana'antu da dama tilas su rage ma'aikatansu yadda suka kai ga ƙarancin waɗanda zasu riƙa kula da ɓengaren yaƙi da cin hanci da rashawa a aiyukan su na yau da kullum.

Sylvia Schenk tace, ba ko wace dangantakar ciniki ce ta kan haɗa da cin rashawa ko karɓar toshiyar baki ba. To amma ɓengaran da wannan al'amari yafi ƙarfi cikin sa, shine ɓengaren gine-gine, inda bayan ma haɗin baki a ɓengaren aiyukan kamfanonin, akan kuma sami ɓullowar wannan matsala.

Tun dai shekarar 1995, wannan ƙungiya ta Transparency, take fitar da iri-irin wannan rahoto a ko wace shekara inda ake bada maki daga goma zuwa ƙasa, wato daga ƙasashe mafi ƙarancin ci hanci, zuwa ƙasashen da cin hancin yayi musu katutu.

Rahoton ya nunar da cewa, daga cikin wa'innan ƙasashe 180 a ƙalla ƙasashe arba'in da tara ne(49) suke da dama wajan matsalar cin hanci.

ƙasar faransa na sahu na 24 yayin da ƙasar jamus ke sahu na 14 Belgium na sahu na 12.

Idan aka dubi ƙasashen Afrika, ƙasar Ghana na sahu na 69 yayin da ƙasar Senegal ke kan sahu na 99 a fannin cin hanci, sai gungun ƙasashe kamar su jamahuriyar Benin, Gabon Gambiya da jamahuriyar Nijar na sahu na 106 su kuma Mali da Togo na sahu na 111, ƙasar Najeriya na cikin gungun ƙasashen kamar su Libiya ,Mauritania da ƙasar Uganda inda suke a sahu na 130.

Ƙasashen da suke sahu na ƙuta da cin hancin yayi wa katutu, sune ƙasashen, Tchadi, Iraki Sudan, Myanmar, Afghanistan da Somaliya da a wannan karo ma itace sahun gaba wajan matsalar cin hanci da rashawa inda take da maki ɗaya da ɗigo ɗaya.

Idan aka ce ƙasashe matalauta ne da masu fama da yaƙi ke kan gaba wajan matsalar cin hanci da rashawa, ƙungiyar daga nata ɓengare ba ta bar sauran ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziki ba, a cewar shugabar wannan ƙungiya ta Transparency Int Huguette Labelle bai kamata kuɗaɗan daake samu ta mugunyar hanya su rinƙa samun mafaka a wa'innan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ba, a cewar ta ya kamata, a dakatar da wannan mumunar ɗabi'ar.

A wurare da dama dai inda ake bayar da manyan kwangila bincike ya nunar da cewa, anfi saurin fuskantar matsalar cin hanci inda yan kwagila ke neman bayar da wani abu dan su samu babbar kwangila, yayin da wasu ke bayanin cewa, lalle ne shugabannin kula da kwangila basa cika aikin su yadda ta kamata, muddin ba'abasu wani abu ta hanyar cin hanci ba.

Mawallafi: Salissou Boukari

Edita: Hauwa Abubakar Ajeje