Rahoto kan kisan da aka yi a Marikana na Afirka ta Kudu | Siyasa | DW | 26.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoto kan kisan da aka yi a Marikana na Afirka ta Kudu

Shugaban Afirka ta Kudu ya gabatar da rahoto bincike kan kisan da 'yan sanda suka yi wa ma'aikatan hakar ma'adanai

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta kudu ya gabatar da sakamakon bincike da aka gudanar dangane da kisan da jami'an 'yan sanda kasar suka yi, a lokacin boren ma'aikatan wata ma'akatar hakar ma'adinai da ke Marikana.

Kusan shekaru uku da aiwatar da kisan a kofar ma'aikatar hakar ma'adinan na Marikana da ke Afrika ta kudun, ana iya cewar babu abin da ya sauya a wannan gari da ke fama da wahalhalu na rayuwa tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata. Duk da dumbin albarkatun kasa da Allah ya hore wa wannan gari dai, a bayyane yake cewar har yanzu al'ummarta na rayuwa cikin matsanancin talauci.

Da yake gabatar da sakamakon binciken, Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta kudu, ya zargi kamfanin hakar ma'adinai da rashin daukar matakin da ya dace, a yayin boren ma'aikatan na watan Augustan shekara ta 2012. Duk da cewar rahotan ya soki manufofin kamfanin na Lonmin dangane da gaza shawo kan matsalolin rayuwa da rashin gidaje wa ma'akatanta, akasarin al'ummar Marikana na ganin cewar babu abin da rahotan zai sauya dangane da wannan batu.

Kasar ta Afirka ta kudu tana fama da matsalar fushin ma'aikatan ma'adinai sakamakon rashin kyan yanayi na aiki da rashin kulawa da rayuwarsu, shekaru 20 bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata.

Tuni dai 'yan adawa na Afrika ta kudu suka nuna dan yatsa kan manyan ma'aikatan gwamnati da suka hadar da mataimakin shugaban kasa Cyril Ramaphosa, a matsayin wadanda ke da alhakin kisan da 'yan sandan suka yi a Marikana.

Sauti da bidiyo akan labarin