Raguwar sojin Rasha kusa da Ukraine | Labarai | DW | 13.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Raguwar sojin Rasha kusa da Ukraine

Rundunar sojin Ukraine ta ce an samu raguwar sojin Rasha a yankunan da 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha da dakarun gwamnatin kasar ke tafka fada.

Andriy Lysenko da ke magana da yawun hukumar tsaron kasar ya ce da safiyar Litinin din nan galibin sojin Rashan da aka girke a wasu sansanoni da ke Ukarine sun koma sansaninsu na asali da ke cikin Rasha.

Wannan dai na zuwa ne bayan da a karshen mako shugaban Rashan Vladmir Putin ya bada umarnin janye dubban sojin kasarsa da aka tura kusa da kan iyakar kasar da Ukraine.