Raguwar kwararar ′yan gudun hijira zuwa Turai, inji kungiyar NATO | Labarai | DW | 21.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Raguwar kwararar 'yan gudun hijira zuwa Turai, inji kungiyar NATO

Yawan 'yan gudun hijira da ke bi ta tekun Aegean zuwa Turai ya ragu sosai, sai dai dole a cigaba da dakile hanyoyin masu safarar mutane.

Sakatare Janar na kungiyar kawancen tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce yawan bakin haure da kuma 'yan gudun hijira da ke tsallaka tekun Aegean daga Turkiyya zuwa Turai ya ragu matuka amma masu safarar mutane ka iya canja hanyoyin da suke bi. Saboda haka bai kamata hukumomi su yi saurin rage matakan tsaro da suke dauka da nufin dakile kwararar 'yan gudun hijirar ba. A lokacin da yake jawabi a Ankara babban birnin kasar Turkiyya shugaban na NATO Jens Stoltenberg ya ce bisa bayanan da kungiyar ta tattara kwararar 'yan gudun hijira ta ja da baya bayan da jiragen ruwan NATO suka fara siniri a tekun na Aegean.

"Turkiyya na daukar matakin magance salon fataucin 'yan Adam, kuma alkalumma daga kungiyoyin kasashe dabam-dabam sun tabbatar cewa yawan 'yan gudun hijirar da ke ratsawa tekun Aegean na raguwa yanzu."