1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farashin mai ya sauko a Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
February 20, 2019

A cewar Lai Mohammed kungiyar masu siyar da albarkatun mai me zaman kanta (IPMAN) ta rage farashin daga Naira145 duk lita.

https://p.dw.com/p/3Djka
Nigeria Tankstelle in Lagos
Hoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

Kungiyar da ke siyar da albarkatun mai a Najeriya ta bayyana rage farashin man fetir a kasar ta yaddda al'umma za su samu damar tafiye-tafiye ta yadda za su yi zabe a ranar Asabar mai zuwa, mako guda bayan da aka dage zaben kasar kamar yadda ministan yada labarai ya bayyana a wannan Laraba.

A cewar Lai Mohammed kungiyar masu siyar da albarkatun mai me zaman kanta (IPMAN) ta rage farashin daga Naira145 duk lita zuwa Naira 140. Wannan ragin farashi dai zai samu ne tsakanin ranakun 21 ga watan nan na Fabrairu zuwa 25 ga watan na Fabrairu. Ranakun da masu zaben za su iya amfani da su su je su yi zabe su koma wuraren aikinsu ko kasuwancinsu.