Wannan shirin rediyo na koyar da harshen Jamusanci mai suna "Radio D", an shirya shi ne domin masu koyo wadanda ba su da wata masaniya a kan harshen, kuma ya kunshi mataki na A1 da na A2 a bisa Tsarin Koyar da Harsuna na Tarayyar Turai. Wannan shiri zai taimaka muku gogewa wajen sauraro da fahimta cikin sauki. Kuna iya sauraron duk jerin shirye-shiryen, sannan kuma kuna iya karanta shi a rubuce a wannan shafi. An kirkiro wannan shiri na Radio D ne da hadin gwiwar Cibiyar Goethe.
Matakai: A1, A2
Kafar sauraro: Sauti, Rubutu (za a iya saukar da shirin ta nan)
Harsunan gabatarwa: Jamusanci | Turanci