Ra′ayoyin jaridun Jamsu kan nahiyar Afirka a wannan makon. | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 04.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ra'ayoyin jaridun Jamsu kan nahiyar Afirka a wannan makon.

Muhimman jigogin da jaridun Jamus suka fi mai da hankali a kansu game da nahiyar Afirka, sun haɗa ne da warware rikicin da aka yi tsakanin Cadi da bankin duniya, da halin da akke ciki a Somaliya, da haɓakar asarar rayukan baƙin haure daga nahiyar, masu yunƙurin shigowa Turai ta ruwa........,

Baƙin haure daga nahiyar Afirka cikin kwalekwale.

Baƙin haure daga nahiyar Afirka cikin kwalekwale.

Cim ma wata madafa da aka yi, tsakanin bankin duniya da ƙasar Cadi a kan yadda ƙasar za ta yi amfani da kuɗaɗen da take samu daga sayad da man fetur, da rikicin ƙasar Somaliya, da asarar rayukan da ake ta ƙara samu na baƙin haure daga nahiyar Afirka da ke ta yunƙurin shigowa Turai ta hanyar ruwa, na cikin muhimman batutuwan da jaidun Jamus suka yi sharhohi a kansu game da nahiyar Afirka.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta dubi warware rikicin da akka yi ne tsakanin ƙasar Cadi da bankin duniya, game da yadda ƙasar za ta dinga amfani da kuɗaɗen da take samu daga kasuwancin man fetur. Bisa cewar jaridar dai, gwamnatin Cadin, ta amince ta yi amfani da kashi 70 cikin ɗari na kasafin kuɗinta wajen aiwatad da shirye-shiryen rage yawan talauci a ƙasar. Daga kuɗaɗen da take samu a cinikin man fetur dai, gwamnatin za ta yi amfani da su wajen inganta harkokin kiwon lafiya, da na ilimi da kuma gina tituna da samad da makamashi da dai sauransu. Bayan tattaunawar da ya yi da shugaba Idrid Deby na ƙasar Cadin, shugaban bankin duniya Paul Wolfowitz, ya ce wannan wani gagarumin mataki ne na ci gaban ƙasar.

Yanzu dai, inji jaridar, bankin duniyar zai sa ido ne ya ga ko shugaba Debyn zai cika alkawarin gwamnatinsa. Rikici tsakanin ɓangarorin biyu ya ɓarke ne, bayan da shugaba Deby ya ba da sanarwar cewa, ba zai bi ƙa’idojin da bankin duniya ya shimfiɗa ba wajenyin amfani da arzikin ƙasar. A maimakon haka, zai sayo makamai ne ga rundunar sojinsa. Wannan matakin dai, inji jaridar, ya saɓa wa yarjejeniyar da Cadin ta cim ma da bankin duniyar a ƙarshen shekarun 1990, kafin bankin ya zuba jarin gudanad da ayyukan shimfiɗa bututun man fetur mai tsawon kusan kilomita dubu, da ake fid da da man da ake haƙowa a ƙasar zuwa kasuwannin duniya. Sabili da hakan ne a farkon wannan shekarar, bankin duniyar ya tsai da bai wa Cadin rance da kuma hana ta taɓa wasu kuɗaɗen haraji da kamfanonin haƙo man fetur ɗin ke biya a wani asusu na musamman da ke London.

JaridarNeue Zürcher Zeitung kuma ta dubi halin da ake ciki ne a ƙasar Somaliya inda ta yi tambayar ko da gaske ne sojojin Habasha sun janye daga ƙasar? Bisa rahotannin da ke iso mata dai, inji jaridar:-

A ƙarshen makon da ya gabata, ba a sake ganin dakarun Habasha a Baidoa, hedkwatar gwamnatin wucin gadin ƙasar Somaliyan ba kuma. Bisa cewar mazauna yankin dai, dakarun Habashan sun janye gaba ɗaya daga ƙasar. Wani kakakin gwamnatin wucin gadin ma, ya ƙaryata rahotannin da kafofin yaɗa labarai suka yi ta bugawa a kan wannan batun, na cewa sojojin Habashan sun kutsa cikin Somaliyan. Ya ƙarfafa cewa, babu wani sojan Habasha da ya taɓa sanya ƙafarsa a harabar Somaliyan.

Sai dai kawo yanzu, babu wanda ya iya tabbatad da hakan, inji jaridar. Ƙungiyoyin islaman da ke riƙe da birnin Mogadishu dai, sun ƙaurace wa shawarwarin zaman lafiya tsakaninsu da gwamnatin wucin gadin Somaliyan ne, saboda zargin da suke yi mata na amincewa da shigowar dakarun Habasha a ƙasar. A wani lokaci ma sai da shugaban ƙungiyoyin islaman, Scheikh Hassan Ɗahir Aweys, ya yi barazanar ƙaddamad da jihadi a ƙasar, don yaƙan dakarun Habashan. Har ila yau dai, ƙungiyoyin islaman ba su yarda cewa Habashan ta janye dakarunta ba.

Jaridar ta ƙara da cewa, girke dakarun da Habashan ta yi a Baidoa ya sa ’yan majalisar Somaliyan sun gabatad da wani mataki na tsige Firamiyan ƙasar Ali Mohammed Gedi. A wata muhawarar da suka yi, ’yan majalisa ɗari da 26 ne suka ka da ƙuri’ar sauke Firamiyan daga muƙaminsa. Sai dai duk da haka, ba su sami rinjayi ba. Bayan ka da ƙuri’ar ma, sai da aka sami wani hargitsi a zauren taron ’yan majalisar a Baidoa, inda da kyar ne masu kare lafiyar Firamiya Gedi, suka iya fida da shi daga gun.

Asarar rayukan da ake ta ƙara samu, na ɗimbin yawan bakin haure daga nahiyar Afirka da ke ta yunƙurin shigowa Turai ta ruwa, ita ce jigon sharhin da jaridar die Tageszeitung ta yi kan nahiyar a wannan makon. Jaridar ta ce a cikin daren ran juma’ar da ta gabata, jirgin ruwan jami’an tsaron iyakar tekun ƙasar Italiya, ya ceto wasu mutane 14 daga nitsewa da kwalekwalensu a kudancin tsibirin nan na Lampedusa. Mutanen dai sun bayyana cewa, sun fi haka yawa. Amma 13 daga cikinsu sun mutu. Kuma sun jefa gawawwakinsu cikin teku. Tun kwanaki 20 ne dai mutanen suka taso cikin ɗan ƙaramin kwalekwalen daga Libiya. Ba da daɗewa bayan tasowarsu ba ne suka rasa alƙiblarsu. A lokacin da aka gano kwalekwalen da suke cikin dai, inji jaridar, an sami mutane biyu a sume, waɗanda a halin yanzu ake ta ƙoƙarin farfaɗo da su a asibiti. Duk waɗanda aka ceton dai daga ƙasashen Mali, da Eritrea da Masar suke. A ƙarshen makon da ya gabata ma, sa da wani jirgin jami’an tsaron iyakar Italiyan ya ceto wasu mutane 13 kuma kusa da gaɓar tekun ƙasar Malta, yayin da wasu 17 kuma suka nitse kafin a iya kai gare su. 8 daga cikinsu dai yara ƙanana ne, inji jaridar.

 • Kwanan wata 04.08.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvPj
 • Kwanan wata 04.08.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvPj