Putin ya ce darajar takardar kudin Rasha za ta farfado | Labarai | DW | 18.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Putin ya ce darajar takardar kudin Rasha za ta farfado

Shugaban na Rasha ya dora laifin karayar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a kan takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Rasha.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce yana da kyakkyawan fatan cewa tattalin arzikin kasar zai farfado kuma darajar taradar kudinta wato Rubel ita ma za ta daidaita. Shugaban na Rasha ya fada wa wani taron manema labarai na karshen shekara a birnin Mosko cewa tsanani za a kwashe tsawon shekaru biyu ana fama da wannan matsala ta tattalin arziki. Ya ce tuni babban bankin kasar da kuma gwamnati sun dauki matakan da suka dace, ko da yake an dan makara. Putin ya ce koma-bayan tattalin arzikin dai ya faro ne saboda katsalandar kasashen waje, yana mai cewa takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Rasha dangane da rikicin Ukraine ke da alhakin kimanin kashi 30 cikin 100 na matsalolin tatalin arzikin. Ya ce za a rage yawan dogaro kan man fetir.